Wannan kundi ya shafi wasu kayayyaki daban daban, kamar su tofa, inabi, lemun zaki, 'ya'yan itatuwan wurare masu yanayin zafi da sauransu, in ji Mashudu Silimela, mai bada shawara kan harkokin noma a ofishin jakadancin Afrika ta Kudu dake Beijing.
Bangarorin biyu sun dauki niyyar yin musanyar bayanai kan rigakafi da bincike, tsara dokoki, shiga kasuwanni, kyautata kasuwanni da bunkasa kasuwanni, fasahohin zamani da sauran batutuwan dake alaka da hakan, in ji mista Willem Bestbier, shugaban FruitSA.
Mista Silimela ya bayyana cewa sanya hannu kan wannan yarjejeniya zai kafa wani yanayi mai kyau domin bunkasa kasuwancin 'ya'yan itatuwa tsakanin kasashen biyu, da kuma kafa wani tsarin dangantaka mai karfi tsakanin FruitSA da CIQA.
Afrika ta Kudu, babbar kasa ce dake fitar da lemun zaki a duniya, kana kuma kasar Sin kasa ce dake shigo da lemun zakin Afrka ta Kudu sosai a yankin Asiya. (Maman Ada)