in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta taimakawa kasashen Afirka kafa asusun magance matsalar sauyin yanayi
2017-09-28 09:39:36 cri

Jami'in kula da shirin kare muhalli na MDD (UNEP) Richard Munang, ya bayyana shirin MDDr na taimakawa gwamnatocin kasashen Afirka kan yadda za su kafa asusun tunkarar matsalar sauyin yanayi, ta yadda za su inganta matakan shiyyar na kawar da wannan matsala.

Jami'in na MDD wanda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua hakan a birnin Nairobi na kasar Kenya, ya ce, yanzu haka nahiyar Afirka tana bukatar dala biliyan 50 a ko wace shekara domin magance matsalar sauyin yanayin wadda yanzu haka ta yiwa nahiyar daurin hohon goro.

Bayanai na nuna cewa, shirin na UNEP yana kokarin kafa asusun yaki da matsalar sauyin yanayi a yankin Makueni, mai nisan kilomita 130 kudu maso yammacin Nairobi, fadar mulkin kasar Kenya.

Yankin na Makueni dai shi ne na farko a nahiyar Afirka da zai kafa irin wannan asusun don magance kalubalen da bangaren jin dadin jama'a da tattalin arziki mai nasaba da matsalar sauyin yanayi.

Bugu da kari, UNEP yana shirin kafa irin wannan asusu a sassa daban-daban na kasashe 40 na Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China