Hukumar ta bayyana haka ne cikin wani rahoto da ta fitar a baya-bayan nan kan yanayin da ake ciki wajen samar da abinci da kula da aikin gona a fadin duniya a bana.
Rahoton ya ce idan kasashe masu tasowa za su iya daidaita ayyukan samar da abinci da sauran sana'o'i masu alaka da shi a yankunan karkara, to akwai yiwuwar su samu damar raya tattalin arzikin yankunansu yadda ya kamata. (Bello Wang)