Bisa wata yarjejeniyar da hukumar FAO da ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin suka kulla a wancan rana, gwamnatin kasar Sin, za ta ware dalar Amurka miliyan 11, daga cikin kudin tallafi da take ba shirin hadin gwiwar kasashe masu tasowa na dala miliyan 80, don taimakawa wasu sabbin shirye-shirye 3 karkashin tsarin nan na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, ciki har da taimakawa kasashen aiwatar da yarjejeniyar kare itatuwa da bishiyu.
A cewarta, mataimakiyar sakataren janar ta hukumar FAO mai kula da batutuwan da suka shafi yanayi da albarkatun kasa, Madam Maria Helena Semedo, shirin raya hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa ya taka muhimmiyar rawa wajen mai da su zama masu cude-ni-in-cude-ka.
Jami'ar ta ce bisa kokarin bangarori daban-daban, musamman ma tallafin da kasar Sin ta bayar, an samu ci gaba sosai a wannan shiri, inda ta ce zai taimaka matuka, ta fuskar samar da isashen abinci a duniya, da tabbatar da samun ci gaba mai dorewa. (Bello Wang)