Mr. Guterres ya ce, ana mutunta 'yancin kasar Iraki, don haka, ya kamata a warware sabanin dake tsakanin gwamnatin tsakiyar kasar Iraki da gwamnatin yankin Kurdawa ta hanyar siyasa.
Ya kuma nuna fatan cewa, lamarin ba zai haifar da illa ga MDD wajen gudanar da ayyukanta a yankin Kurdawa ba, a sa'i daya kuma, ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta ci gaba da nuna goyon baya ga MDD wajen gudanar da ayyukanta a kasar yadda ya kamata.
A jiya Litinin ne, Kurdawan Iraki sun kada kuri'un neman 'yancin cin gashin kan yankinsu, lamarin da ya gamu da rashin amincewa kwarai da gaske daga gwamnatocin Iraki da Turkiya da kuma Iran.
Bugu da kari, kasar Amurka da kungiyar tarayyar kasashen Turai sun nuna goyon bayansa kan dunkulewar kasar Iraki baki daya. (Maryam)