in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Iraqi na kokarin yi wa Tal Afar dake hannun kungiyar IS kawanya
2017-08-22 10:10:35 cri
Dakarun Iraqi dake yaki da mayakan IS, sun kara kwace Karin kauyuka da muhimman yankuna, a yayin da suke kara matsawa don yi wa mayakan IS kawanya a garin Tal Afar da yankuna dake kewaye da shi.

Wata sanarwa da Lt. Gen. Abdul-Amir Yarallah na rundunar hadin gwiwa dake yaki da mayakan ya fitar, ta ce dakarun da jami'an tsaron sassan Hashd Shaabi, su tunkari garin ta hanyoyi da dama, ta kauyuka dake kusa da Tal Afar wanda ke da nisan kilomita 70 daga barin yammacin birnin Mosul da aka 'yanto a baya-bayan nan, inda suka kwace iko da kauyuka 7 da kuma babbar hanyar al-Kasak dake gabashin Tal Afar.

Wannan yunkuri wani bangare ne na aikin da Firaministan kasar Haider Al-Abadi ya ayyana da safiyar ranar Lahadin da ta gabata, wanda ke da nufin kwace iko da garin Tal Afar dake arewacin kasar da kuma yankunan dake kewaye da shi daga hannun mayakan IS. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China