Jakadan Sin Chen Weiqing, da ministan cikin gidan Iraqi Qasim al-Araji, ne suka jagoranci bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin kasashen biyu.
Tallafin wanda kasar Sin zata samar, zai taimaka wajen aiwatar da shirin bada kayayyakin jinkai a kasar Iraqin.
Chen Weiqing ya taya gwamnatin Iraqi murna bisa nasarar data cimma a yaki da ta'addanci, kana yace gwamnatin Sin zata cigaba da karfafa gwiwa ga kamfanonin kasar Sin dasu shiga aikin gine ginen farfado da kasar Iraqin bayan yaki.