Mataimakin ministan kula da 'yan gudun hijira da bakin haure na kasar Iraki Jasim Al Attiyah ya bayyana cewa, sansanin yana garin Hamam al-Alil ne mai nisa kilomita 20 kudu da birnin Mosol. Mutane da dama daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su sun rasa takardunsu na asali, wannan ya sa sojojin tsaron kasar suke tantance asalinsu a kokarin tabbatar da kasashensu.
Mr. Attiyah ya bayyana cewa, hukumomin kasar suna shirya kai su wani sansani na daban, ma'aikatar kula da 'yan gudun hijira da bakin haure ta kasar ta samar musu da abinci da jinya.
Wani jami'in tsaro a birnin Mosol ya bayyana cewa, game da mambobin kungiyar IS da aka kama iyalansu, wasu sun mutu a cikin yakin kwato Tal Afar, wasu kuwa sun mika makamansu ga sojojin gwamnatin kasar ko dakarun Kurdawa. (Zainab)