in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata kotu a Iraqi ta yi fatali da batun kuri'ar raba gardama na ballewar yankin Kurdistan
2017-09-19 11:10:58 cri
Kotun kolin kasar Iraqi a ranar Litinin ta dakatar da shirin kuri'ar raba gardama na neman cin gashin kai na yankin Kurdistan wanda aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga wannan watan.

A ranar 12 ga watan Satumba ne majalisar dokokin Iraqi ta kada kuri'ar kin amincewa da kuri'ar raba gardama na neman ballewar yankin na Kurdish, amma 'yan majalisar dokokin daga yankin na Kurdish sun fice daga zauren majalisar don nuna adawa da wannan mataki.

Dama dai batun yancin yankin na Kurdistan yana shan suka daga wasu kasashen duniya sakamakon abin da wasu ke ganin yana iya rage darajar kasar Iraqi, kana sakamakon yadda dakarun Iraqin ke yaki da ta'addanci, ciki har da batun yaki da kungiyar IS mai da'awar kafa daular Musulunci.

Bugu da kari, makwabtan kasashe irinsu Turkiyya, Iran da Syria suna ganin matakin zai iya zama barazana ga tsaron kan iyakokin kasashensu, kasancewar kaso mai yawa na al'ummomin Kurdawa suna zaune ne a wadancan kasashen.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China