Kuma cikin sanarwar da ta fitar, ba ta ambaci daidai lokacin da ta gudanar da wannan aiki ba.
A ranar 10 ga watan Yuli, rundunar sojojin gwamnatin kasar Iraq ta kwace ikon birnin Mosul, fadar mulkin lardin Ninewa, wanda yake da nisan kilomita dari 4 daga birnin Bagadaza, babban birnin kasar Iraqi. A watan Yunin shekarar 2014, kungiyar IS ta mamaye birnin Mosul, sa'an nan, kungiyar ta mai da birnin babban sansaninta mafi girma a duk fadin kasar ta Iraqi.
A halin yanzu, sojojin kasar Iraqi suna taruwa a yankin dake yammacin birnin Mosul, domin shiryawa game da farmakin da za su kaddamar domin kwace ikon birnin Tal Afar. Birnin Tal Afar, yana yammacin birnin Mosul, wanda yake da nisan kilomita 70 daga birnin, kuma shi ne sansani na karshe na kungiyar IS dake cikin lardin Ninewa. (Maryam)