A jiya ne rundunar mayakan saman kasar Iraki suka kai wani hari a garin al-Qaim da ke lardin Anbar na yammacin kasar, harin da ya halaka 'yan tawayen IS 68.
Garin al-Qaim yana dab da bakin iyakar kasashen Iraki da Syria. Tun a shekarar 2014 ne 'yan tawayen IS sun kwace garin da kuma garuruwan Aana da Rawa da ke kusa da shi. Yanzu wadannan garuruwa 3 su ne na karshe da ke hannun 'ya tawayen na IS a lardin Anbar. (Tasallah Yuan)