in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutanen Iraqi na adawa da sabuwar dokar zaben kasar
2017-08-05 13:28:08 cri
Al'ummar kasar Iraqi da dama ne suka taru a filin 'yantar da al'umma dake tsakiyar babban birnin kasar wato Baghdad, domin nuna adawa da sabuwar dokar zabe da majalisar dokokin kasar ta zartas a kwanakin baya.

Mutanen sun taru ne a jiya Jumma'a, karkashin jagorancin Moqtada al-Sadr, babban shugaban kungiyar Shi'a a Iraqi, wanda ya yi zargin cewa, dokar zaben da majalisar dokokin ta zartas, ta ba da damar sake lashe zabe ga 'yan majalisar wadanda suka taba karbar rashawa, lamarin da ya ce, zai yi nakasu ga ayyukan yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Masu adawar sun yi ta daga tutar kasar, suna masu ihun suna cewa "muna kin cin hanci da rashawa".

A nasu bangaren, sojojin Iraqi sun toshe tsakiyar birnin Baghdad, inda suka kuma dauki matakan kiyaye tsaro a wurin dandazon jama'ar.

A baya bayan nan ne majalisar dokokin kasar Iraqi, ta zartas da dokar zabe da za a yi a lardunan kasar cikin shekara mai zuwa, inda wasu ke ganin cewa, dokar ta nuna fifiko sosai ga manyan jam'iyyun majalisar dokokin kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China