in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da mayakan IS 2,000 ne aka halaka a Tal Afar na Iraki
2017-09-03 17:04:15 cri
Rundunar sojin Iraki, ta ce ta kashe mayakan kungiyar IS sama da 2,000 tare da 'yan kunar bakin wake 50, yayin wani farmaki da ta kai musu a kokarinta na kwace iko da yankin Tal Afar dake yammacin birnin Mosul.

Yayin wani taron manema labarai da aka watsa ta gidajen talabijin, kwamandan rundunar hadin gwiwa dake yaki da kungiyar IS Lt. janar Abdul Amir Yarallah, ya ce jimilar mayakan IS da matakin sojin ya rutsa da su tsakanin ranar 20 zuwa 31 ga watan Augustan da ya gabata, ya kai sama da 2,000 da 'yan kunar bakin wake sama da 50, inda kuma sojojin suka kwance tare da lalata motoci dauke da bama-bamai 77 da gine-gine da aka boye bama-bamai a cikinsu 71 da kuma bama-baman da aka dana a gefen hanyoyi 990.

Kwamandan ya ce, sama da mayakan Iraqi 40,000 da suka kunshi sojoji da jami'an 'yan sandan kasa da na sashen yaki da yan ta'adda da mayakan rundunar Hashd Shaabi ne suka kai famakin bisa samun goyon baya daga jiragen yakin Iraqi da na kawancen kasashen waje.

Har ila yau, Lt. Janar Yarallah ya ce, kimanin dakarun Iraqi 115 ne suka yi mutuwar shada, inda wasu 679 suka samu raunuka yayin arangamar da aka shafe kwanaki 12 ana yi da nufin 'yanto Tal Afar da yankunan dake kewaye da ita, ciki har da biranen Mahalabiyah da Ayadhiyah. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China