Gidan telabijin na kasar Iraki ya ambato kalaman babban jami'in jam'iyyar kawancen Kurdistan Pavel Talabani yana cewa, bayan da manyan jam'iyyun yankin suka yi bincike kan dukkan shawarwarin da aka basu, shawarar jinkirta kada kuri'ar da kasar Amurka da Birtaniya da sauran kasashe da kuma MDD suka bayar ta fi dacewa ga jama'ar Kurdistan.
Game da wannan batu, wani jami'in ofishin shugaban yankin Kurdistan ya bayyana cewa, maganar Talabani ra'ayi ne na kashin kansa, bai wakilci ra'ayin gwamnatin yankin ba, za a kada kuri'un bisa shirin da aka tsara.
Da ma,gwamnatin yankin Kurdistan da gwamnatin tsakiya ta kasar Iraki babu kyakkyawar hulda a tsakaninsu, bangarorin biyu suna da matsaloli kan mallakar yankuna da dama, musamman jihar Kirkuk dake da albarkatun man fetur. (Zainab)