in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A rusa daraktocin hukumar kula da muhalli ta Tanzaniya
2017-07-18 09:37:44 cri

Rahotanni daga kasar Tanzaniya na cewa, mahukuntan kasar sun sanar da rusa daraktocin hukumar kula da muhalli ta kasar bisa zarginsu da aikata laifin cin hanci.

Karamin minista a ofishin mataimakin shugaban kasa mai kula da hukumar January Makamba ya ce, an dauki wannan mataki ne sakamakon zargin da ake yiwa hukumar da karbar na goro yayin ba da takardar shaidar tsaftar muhalli da kuma jinkiri na gaira babu dalili yayin da take tantance tsaftar muhalli.

Ministan ya kara da cewa, daukar wannan mataki zai baiwa hukumar damar gudanar da ayyukanta na kare muhalli a fadin kasar yadda ya kamata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China