Kasar Sin tana fuskantar kalubaloli a wannan fanni, ciki har da matsalar kafewar ruwa, zaizayar kasa da gurbatacciyar iska, jami'in na hukumar tsara cigaba da kwaskwarima ta kasar Sin, wanda ba'a bayyana sunansa ba shi ne ya yi wannan tsokaci.
A cewar jami'in, kasar Sin tana da yankuna da yawansu ya kai murabba'in kilomita miliyan biyu da dubu 95 wanda ke fuskantar matsalolin kafewar ruwa da zaizayar kasa, da kuma yankuna da fadinsu ya kai murabba'in kilomita miliyan 1, da dubu 73 wadanda ke fama da matsalar hamada.
Domin inganta muhalli, ya kamata kasar Sin ta kara karfafa dokoki da suka shafi amfani da filaye da kuma albarkatun kasa, kuma ta aiwatar da tsarin inganta shirin shuke shuke na masana'antu, in ji jami'in.
A farkon wannan shekarar, mahukuntan kasar Sin suka gabatar da wasu ka'idoji na "red line" game da dabarun kiyaye mahallin halittu wanda zai tabbatar da kare wasu yankunan kasar. Ana son cimma wannan buri nan da shekarar 2020.
A ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2015, kasar Sin ta amince da wata doka da ta shafi tsaron kasa, inda aka bayyana ranar 15 ga watan Aprilu a matsayin ranar wayar da kan jama'a game tsaron kasa. (Ahmad Fagam)