Jami'in na Najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin taron bita kan sauyin yanayi wanda aka shirya a birnin Abeokutan jihar Ogun dake shiyyar kudu maso yammacin kasar.
Ya kara da cewa, gwamnatin kasar za ta aiwatar da wani shiri na musamman na NDC a takaice wanda zai taimaka wajen rage adadin hayaki mai gurbata muhalli da duniya ke fitarwa wanda zai kai matsayin digiri 2 a ma'aunin celsius.
Ya ce muddin ana son tabbatar da wannan shiri, dole ne a dauki kwararan matakai na ilmantar da al'umma da kuma yin aiki tare da juna tsakanin dukkan bangarori.
Ministan ya ce, domin cimma nasarar shirin na NDCs, gwamnatin za ta fitar da wani daftari wanda zai dinga tafiyar da al'amuran da suka shafi aiwatar da manufofi game da sauyin yanayi.
Ibrahim ya ce tuni aka cimma gagarumar nasara a matakin gwamnatin tarayya da ma'aikatu da hukumomin gwamnati game da batun tinkarar sauyin yanayi.(Ahmad Fagam)