in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardan MDD ya yi kira da a sake gina dangantakar dake tsakanin bil Adama da muhallin duniya
2017-06-06 11:12:33 cri
A jiya Litinin ne, Babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya yi kira da a sake gina dangantakar dake tsakanin bil Adama da muhallin duniya.

Mr. Guterres ya yi wannan kiran a jawabin da ya gabatar albarkacin ranar muhalli ta duniya, wato ranar 5 ga watan Yunin ko wace shekara. Taken rana ta bana dai ita ce "dangantakar dake tsakanin bil Adama da muhallin duniya".

Mr. Guterres ya bayyana cewa, idan har babu muhalli mai tsabta, to ba za a iya kawar da talauci, da samun wadata a duniya ba.

Haka zalika ya ce, ya kamata kowa ya sauke nauyinsa a fannin kiyaye muhallinmu, kuma za mu iya cimma wannan burin ta hanyar rage amfani da abubuwan roba, rage tafiya da motoci, rage bata abinci da kuma tuna wa kowa batun kare muhallinmu.

A watan Oktoba na shekarar 1972 ne dai, aka zartas da kuduri a babban taron MDD, inda aka mai da ranar 5 ga watan Yunin ko wace shekara a matsayin ranar muhalli ta duniya, kuma tun daga shekarar 1974, hukumar kiyaye muhalli na MDD ta fitar da take a ko wace ranar muhalli ta duniya ta ko wace shekara, tare da yin wasu aikece-aikace da dama dangane da wannan take. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China