A yayin taron, Li Keqiang ya bayyana cewa, cikin 'yan shekarun nan, ana ci gaba da samun ci gaban hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da bangaren Turai, inda suka dukufa wajen aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris domin karfafa hadin gwiwar bangarorin biyu wajen fuskantar sauyin yanayin duniya. Haka kuma, sun dukufa wajen aiwatar da jadawalin samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030, da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin yaki da ta'addanci da kuma kiyaye tsaro.
Bugu da kari, Li Keqiang ya jaddada cewa, bisa yarjejeniyar da aka kulla kan shigar da kasar Sin cikin kungiyar cinikayya ta duniya ta WTO, ya kamata bangarorin da abin ya shafa su aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, ganin cewa nauyi ne dake kansu, da kuma ka'idojin kasa da kasa da ya kamata a martaba. Haka zalika, za a iya warware sabanin dake tsakanin kasar Sin da bangaren Turai ta hanyar yin shawarwari a tsakanin bangarorin biyu, ko kuma a tsakanin bangarori daban daban da abin ya shafa. (Maryam)