A yayin tattaunawar, bangarorin biyu sun amince da kara bunkasa mu'ammala da juna, game da batutuwan duniya, da ci gaba da sa kaimi ga kyautata tsarin tafiyar da harkokin duniya, da bunkasar kasashe bisa daidaito mai dorewa.
Bangarorin biyu sun ce za su ci gaba da kokari tare, don sa kaimi ga samun sabon ci gaba, a yayin taron koli na kungiyar G20 da zai gudana a birnin Hamburg, bisa tushen taron kolin kungiyar na Hangzhou. Kaza lika bangarorin biyu sun amince da sa kaimi ga aiwatar da yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi, da ajandar samun bunkasuwa mai dorewa nan da shekarar 2030, da kuma fadada hadin gwiwarsu a fannin kiyaye tsaro.
Har wa yau, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan kasa da kasa, da na yankuna, ciki har da batun Syria, da na nukiliyar Iran, da yanayin da ake ciki a zirin Koriya da sauransu. (Zainab)