Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada manufar kasar Sin ta goyon bayan dunkulewar kasashen Turai. Mr. Li ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin, yayin taron shekara shekara da jagororin kasashen biyu ke gudanarwa tsakanin su tun daga shekarar 2004.
Ya ce, Sin na fatan yin hadin gwiwa da kungiyar tarayyar Turai ta EU, wajen ganin an samu karfi na sarrafa al'amuran duniya a sassa daban daban, tare da fadadar tattalin arzikin duniya a yankuna da dama.
Birnin Berlin ne zangon farko da firaministan na kasar Sin ya sauka, cikin ziyarar aiki ta kwanaki 3 da zai gudanar a Jamus da kasar Belgium.
A birnin Brussels, Li Keqiang zai jagoranci taro na 19, na Sin da kasashen Turai tare da shugaban kungiyar EU Donald Tusk, da jagoran hukumar gudanarwar kungiyar ta Turai Jean-Claude Juncker.
Kaza lika zai gana da shugabannin kasar Belgium kafin dawowa kasar Sin.(Saminu)