in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci Sin da EU, da su kara kokarin tabbatar da shawarwari kan batun Syria
2017-04-26 13:38:24 cri
Manzon musamman na kasar Sin mai kula da batun Syria Xie Xiaoyan dake ziyara a cibiyar EU, ya bayyana a ranar 25 ga wata cewa, batun Syria batu ne da kasar Sin da kungiyar EU, da sauran kasashen duniya suke dora muhimmanci kwarai a kansa, kuma mu'amala a tsakanin Sin da EU zai taimakawa wajen tabbatar da warware batun Syria ta hanyar siyasa.

Xie Xiaoyan ya yi hira da 'yan jarida na ciki da wajen kasar a ofishin jakadan kasar Sin dake hedkwatar kungiyar EU. Inda kan yadda za a warware batun Syria, ya ce kasar Sin tana kulawa da fannoni hudu, wato tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da yaki da ta'addanci, da kyautata yanayin jin kai, da kuma sa kaimi ga warware batun Syria ta hanyar gudanar da shawarwari cikin lumana.

Haka zalika kuma, Mr Xie ya jaddada cewa, wadannan fannoni hudu suna hade da juna, wato ba za a iya maida hankali ga kowane fanni guda a kyale sauran fannonin uku ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China