Chang Wanquan ya bayyana a yayin da yake ganawa da Mogherini cewa, a shekarun baya bayan nan, an kiyaye bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da EU yadda ya kamata, da zurfafa hadin gwiwarsu a fannin kiyaye tsaro. Sin tana son hada kai tare da EU don kara zurfafa hadin gwiwa ta yadda za su bunkasa dangantakar dake tsakaninsu.
A nata bangare, Mogherini ta bayyana cewa, EU ta mai da hankali sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, tana kuma fatan za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannin kiyaye tsaro.
A jawabinsa yayin da yake ganawa da ministar tsaron kasar Kenya Chang Wanquan ya bayyana cewa, Sin tana son hada kai tare da kasar Kenya domin bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Kenya zuwa wani sabon matsayi, tare da fadada hadin gwiwa a tsakanin sojojin kasashen biyu, da kiyaye bunkasa dangantakar dake tsakanin sojojin kasashen biyu yadda ya kamata.
A nata bangare, Omamo ta bayyana cewa, kasashen biyu sun dade suna raya dangantakar dake tsakaninsu, kasar Kenya tana fatan raya dangantakar dake tsakaninta da Sin, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin kiyaye tsaron kasa da aikin soja.(Zainab)