in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firayin ministan Sin ya isa Brussels don halartar taron shugabannin Sin da EU
2017-06-02 11:03:00 cri

A ranar Alhamis firayin ministan kasar Sin Li Keqiang, ya isa birnin Brussels domin halartar taron tattaunawa na shugabannin Sin da kungiyar tarayyar Turai EU karo na 19.

Jim kadan bayan isarsa, Li ya bayyana cewa, kasar Sin da EU sun kasance masu taimakawar juna da kuma amfanar da sassa daban daban na duniya game da yanayin dunkulewar tattalin arzikin duniya. A don haka, ya bukaci bangarorin biyu da su hada karfi da karfe wajen tunkarar matsalolin rashin daidaituwar al'amurra na halin da duniya ke ciki ta hanyar hadin gwiwa da juna.

Li ya ce, yana fatan ziyarar tasa za ta kara bunkasa kyakkyawar dangantaka dake tsakanin Sin da EU wajen samun daidaito da kuma zurfafa mu'amala, kana yana fatar bangarorin za su samu kakkarfar dangantaka da hadin kai domin samun ci gaba.

A cewarsa, hadin kai na zahiri da mu'amala dake wanzuwa tsakanin Sin da kasar Belgium ya zamanto abin misali game da irin dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kaasahen Turai sama da shekaru 46 da suka gabata, tun lokacin da kasashen biyu suka kafa huldar diplomasiyya a tsakaninsu.

Kasar Sin a shirye take ta yi aiki kafada da kafada da Belgium domin daga matsayin dangantakar tasu zuwa babban matsayi na kyakkyawar hulda, da aminantaka, da hadin kai domin cin moriyar bangarorin biyu, in ji firaminista Li.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China