in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Jamus sun amince da kara fadada hadin gwiwa karkashin G20
2017-06-02 09:50:49 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ce, kasarsa da Jamus sun amince da burin wanzuwar duniya cikin lumana da hadin gwiwa. Kaza lika sassan biyu na fatan ganin an fadada harkokin cinikayya cikin 'yanci, da zuba jari tsakanin kasashe daban daban, a wani mataki na samar da duniya mai wadata da zaman karko.

Mr. Li Keqiang, ya bayyana hakan ne bayan kammala ziyararsa a kasar Jamus, inda ya gana da shugaban kasar Frank-Walter Steinmeier a jiya Alhamis a birnin Berlin. Yayin ganawar tasu firaminista Li ya ce, kasashen biyu sun amince su fadada hadin gwiwa tsakanin su karkashin kungiyar G20.

Ya ce, Sin za ta taimakawa Jamus, wajen ganin ta karbi bakuncin taron G20 dake tafe cikin watan Yuli a birnin Hamburg cikin nasara. Kuma ya yi fatan taron zai samar da damar cimma daidaito game da wasu harkokin tattalin arzikin duniya.

Firaminista Li ya kara da cewa, duniya na fuskantar rashin tabbas a fannonin siyasar kasa da kasa da tattalin arziki, yayin da a hannu guda ake da burin ganin an hada kai da juna, wajen bunkasa zaman lafiya da ci gaba, tare da dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda.

A nasa bangare Mr. Steinmeier ya yi maraba da ziyarar Mr. Li a kasar Jamus, yana mai jinjinawa sakamakon da aka cimma yayin ziyarar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China