in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin zai ziyarci kasashen Jamus da Belgium
2017-05-28 12:55:28 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira taron maneman labarai a jiya Asabar, inda ta bayana cewa firaministan kasar Sin Li Keqiang, zai kai ziyara kasar Jamus, inda zai yi ganawar shekara shekara da shugabar gwamnatin Jamus, kana zai ziyarci kasar Belgium a hukunce, inda zai kuma jagoranci taron ganawar shugabannin kasar Sin da na kasashen kungiyar tarayyar kasashen Turai ta EU karo na 19 da za a yi a birnin Brussels fadar mulkin kasar Belgium.

Da yake karin haske game da hakan, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Chao, ya bayyana cewa, kasar Sin na fatan karfafa ma'amalar dake tsakaninta da bangarorin da abun ya shafa, domin inganta fahimtar siyasa, da hadin gwiwa tsakanin sassa daban daban, ta yadda za a samar da sabbin damammaki masu kyau, na raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, tsakanin kasar Sin da kasashen Jamus, da Belgium da ma sauran kasashen EU baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China