Kakakin wannan hukumar ta EU ya bayar da sanarwar ce game da yanke hukuncin daurin rai da rai ga Ilham Toxti a ranar 23 ga wata, inda aka cewa, Ilham masani ne da ake girmamawa, inda aka zargi hukuncin daurin rai da rai da aka yanke masa domin laifin neman aware. Sannan an yi kira da a sake shi nan da nan ba tare da wani sharadi ba. Game da wannan, kakakin tawagar Sin dake kungiyar EU ya bayyana cewa, wannan masani a idon EU mutum ne da ya aikata laifi na zuga al'ummomin kasar Sin da su nuna gaba da juna da tada zaune tsaye a kasar. A nahiyar Turai, wadannan ayyuka ma sun sabawa doka. Hukumar shari'a ta kasar Sin ta yanke hukunci ga Ilham bisa doka kuma cikin adalci, inda aka ba shi 'yancin kare kansa. Kakakin ya jadadda cewa, niyyar da kasar Sin ta nuna wajen gina kasa bisa dokoki, da kuma kokarin da kasar ke yi kan wannan batu, ba za su canja ba sabo da tsegumin da sauran bangarorin kasashen waje suka yi. (Zainab)