Li Keqiang ya bayyana cewa, akwai abubuwan rashin tabbas da dama a halin yanzu a fadin duniya, kuma dole ne kasashen Sin da Jamus su ci gaba da mutunta juna, da yi wa juna adalci, da inganta fahimtar juna, da karfafa hadin-gwiwa da mu'amala tsakaninsu, tare kuma da saukaka matakan kasuwanci, ta yadda za'a kara raya huldar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma bada gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya, da inganta hadin-gwiwa, gami da neman ci gaba a shiyyoyi da fadin duniya baki daya.
A nata bangaren kuma, madam Angela Merkel ta ce, kasarta wato Jamus, aminiya ce ta kasar Sin, kana dangantaka da hadin-gwiwa tsakaninsu na bunkasa da kyau.
A halin yanzu, inganta mu'amala da cudanya tsakanin manyan shugabannin Sin da Jamus na da muhimmancin gaske.
Jamus na son kara karfafa mu'amala da hadin-gwiwa da kasar Sin a fannoni da dama, ciki har da zuba jari da cinikayya, da harkokin kudi, da motoci masu amfani da makamashin da ake sabuntawa, da ayyukan kiwon lafiya, da al'adu da makamantansu.(Murtala Zhang)