Wani rahoton da ma'aikatar tsaron kasar Amurka ta fidda a jiya, ya bayyana cewa, a ranar 17 ga watan Maris, sojojin Amurka sun harba wani makami mai linzami samfurin GBU-38 kan wani ginin dake yammacin birnin Mosul, inda dakarun kungiyar IS guda biyu ke ciki, amma, harin ya tarwatsa boma-boman da kungiyar IS ta dasa a cikin ginin a baya, lamarin da ya haddasa rasuwar fararen hula guda 101 dake zama a cikin ginin, da kuma mutane guda hudu dake kusa da ginin.
Haka zalika, wasu ganau sun ce, har yanzu ba a gano inda sauran fararen hula guda 36 dake cikin ginin suke ba.
Mai kula da harkokin binciken wannan lamari, janar Matthew Eisler ya bayyana a yayin taron manema labarai da aka yi a jiya cewa, kafin sojojin kasar Amurka da na kasar Iraki su kai hari a wurin, ba su san akwai fararen hula a cikin ginin ba.
Sojojin kasar Amurka sun fidda wani rahoto a ran 30 ga watan Afrilu, inda suka bayyana cewa, a tsakanin watan Agusta na shekarar 2014 da watan Maris na shekarar 2017, gaba daya sojojin kasar Amurka da sojojin dake kawance sun kai hare-haren sama fiye da dubu 20 a kasar Iraki, wadanda suka haddasa rasuwar fararen hula a kalla guda 352, kana, adadin bai kunshi mutanen da suka rasu cikin harin da aka ambata ba. (Maryam)