Babban jami'in ya tabo wasu batutuwa cikin wani rahoto dake nuna cewa, a yan kwanakin da suka gabata, kungiyar IS ta cigaba da hallaka mutane bisa hukunce hukuncen wasu kotuna da ta kafa na kashin kanta.
Rahotannin sun ce, a ranar Talata data gabata, ISIL ta harbe wasu fafaren hula su 40 a birnin Mosul, bayan da ta zargesu da hada kai da jam'an tsaron kasar Iraqi.
An ce, an ga gawawwakin mutanen ne sanye da tufafi mai launin rawaya, kuma an yi rubutu da launin ja a jikin tufafin dake cewa 'yan leken asirin jami'an tsaron Iraqi, kuma an samu gawawwakin nasu rataye a jikin fala falan wutar lantarki a yankuna da dama na birnin Mosul.
Bugu da kari, da yammacin wannan rana, an harbe wani matashi dan shekaru 27 a yankin Bab al-Jideed dake makwabtaka da tsakiyar birnin Mosul, bayan wani hukuncin da kotun ta ISIL ta yanke masa saboda laifin yin amfani da wayar hannu a Mosul.
Haka zalika, an sake yanke hukuncin rataya kan wasu fararen hula su 6 a ranar 20 ga watan Oktoba a Mosul, bayan an same su da laifin boye layukan wayar hannu, bayan umarnin da ISIL ta bayar na cewa kowane mutum ya mika mata layin wayarsa.(Ahmad)