Rahoton ya ce, mutumin da aka kashe, ya zama jagora na biyu na IS, biyo bayan Abu Bakr al-Baghdadi.
Baya ga Jumaili din, akwai sauran wasu jagororin kungiyar IS wadanda aka kashe a yayin luguden wutan.
Tun a shekarar 2014 har zuwa yanzu, kungiyar IS sun kwace ikon yankunan arewa gami da na yammacin Iraki, tare da akasarin sassan kasar Siriya. A halin yanzu, sojojin gwamnatin Iraki na kokarin kwace ikon birnin Mosul daga hannun IS.
Tuni a ranar 31 ga watan Maris, hukumar leken asirin kasar Iraki ta ce, sojojin saman kasar sun yi luguden wuta kan maboyar dakarun kungiyar IS guda uku a garin Ba'aj dake kan iyakokin Iraki da Siriya, inda suka hallaka 'yan ta'adda 150 zuwa 200, wadanda suka shigo Iraki daga kasar Siriyar.(Murtala Zhang)