A yayin ganawar tasu, sun tattauna kan matakan sojan da za su dauka wajen yaki da kungiyar IS a yankin iyakar kasar Syria, da kuma yadda sojojin kasashen biyu za su gudanar da hadin gwiwa kai tsaye, domin yaki da ta'addanci.
An kuma ruwaito shugaba Bashar na cewa, kungiyoyin ta'addanci abokan gaba ne ga kasashen Syria da Iraq, kuma, sakamakon da kasar Syria ta cimma game da yaki da ta'addanci, za su ba da gudummawa matuka wajen tabbatar da yanayin tsaro, da zaman karko a kasashen biyu.
Haka zalika, wasu rahotanni na cewa, Mr. Falich Fayez ya mika sakon na firaministan kasar Iraq Haider al-Abadi ga shugaba Assad, wanda ke jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwar kasashen biyu a fannin yaki da ta'addanci. (Maryam)