Wata sanarwa da Laftana janar Abdul-Amir Yarallah na rundunar ayyukan hadin gwiwa ya fitar ta bayyana cewa, runduna ta 9 ta sojojin kasar masu sulke da dakarun dake mayar da martanin gaggawa ne suka sake kwace iko da galibin gundumar Mushairfah, ciki har da cibiyar dake tace ruwa.
Yanzu haka dai, sojojin dake arewa da yammcin birnin Mosul sun yiwa mayakan na IS kawanya, ciki har da tsakiyar tsohon birnin.
Tun a watan Yunin shekarar 2014 ne birnin Mosul mai nisan kilomita 400 arewa da birnin Badagaza ya fada hannun mayakan na Is, lokacin da dakarun gwamnati suka gudu suka bar tashoshinsu, lamarin da ya baiwa mayakan na IS damar kwace iko da sassan yankunan arewaci da yammacin Irakin.(Ibrahim)