Sanarwar ta ce dakarun na Hashd Shaabi wanda galibinsu mabiya shi'a ne, sun samu goyon baya daga sojojin kasar Iraki ta hanyar amfani da jiragen sama masu saukar ungulu, sun kwato kauyuka 4 wadanda aka wargaza su a kudancin garin al-Qairwan, wanda yake yankin kudancin Sinjar, mai kimanin tazarar kilomita 100 daga yammacin birnin Mosul.
Sanarwar ta kara da cewa, a arewacin al-Qairwan, dakarun Hashd Shaabi sun kaddamar da hare hare ne cikin dare inda suka katse hanyar kauyukan al-Hatmiya da Tal Qasab, wadanda IS din ke rike da su.
Sanarwar ta ce, da sanyin safiya ne dakarun tsaron suka afkama kauyen Tal Qasab kuma suka kwace ikon garin bayan yin musayar wuta da mayakan na IS, inda suka yi nasarar hallaka mayakan na IS 10 kuma suka lalata wasu motocinsu biyu dake dauke da abubuwan fashewa, sai dai har yanzu ana ci gaba da musayar wuta a yankunan al-Hatmiya.
Dakarun sun kuma kwato kauyukan Ayn Fat'hi da Ayn Ghazal a arewacin garin al-Qairwan, wanda aka kwace daga hannun IS. (Ahmad Fagam)