Sanarwar ta ce, jihar Ninewa, inda birnin Mosul yake, ta zama jihar da ta fi samun rasuwa gami da jikkatar fararen-hula, inda mutane 367 ne suka rasa rayukansu, saura 174 kuma suka jikkata. Sai dai a jihar Bagadaza, inda fadar mulkin kasar wato birnin Bagadaza yake, akwai fararen hula 84 wadanda suka mutu, tare da jikkatar wasu 246.
A nasa bangaren, shugaban Tawagar samar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya dake kasar Iraki, Jan Kubis ya yi Allah da wadannan hare-haren da 'yan kungiyar masu tsattsauran ra'ayi suka kai kan farare-hula da gangan, kana ya yabawa kokarin da gwamnatin kasar Iraki ke yi, na kare fararen-hula lokacin yakin Mosul.
A halin yanzu, sojojin gwamnatin Iraki na ci gaba da gwagwarmaya domin kwace ikon yammacin birnin Mosul, yayin da mayakan kungiyar ta IS ke tsohon garin dake cibiyar birnin Mosul.(Murtala Zhang)