Yanzu sojojin gwamnatin kasar Iraki sun riga sun kwace fiye da kashi 1 bisa kashi 3 na fadin birnin, inda suka matsa kusa da tsoffin ungwanin dake tsakiyar birnin, haka kuma sun katse dukkanin hanyoyin da dakarun IS za su iya bi domin tsira daga birnin.
A daya bangaren kuma, ana samun karin adadin jama'ar birnin dake gudun hijira.(Bello Wang)