Wani hoton bidiyon da aka wallafa kwanan baya ya nuna cewa, akwai yiwuwar wani harin saman da aka kai kan birnin Mosul a karkashin goyon-bayan Amurka , shi ne ya hallaka fararen hula da dama. Rahoton ya ce, an kai harin ne kan wani ginin dake yammacin birnin Mosul, inda fararen hula sama da 230 ke da zama, kuma suke boye a ciki a lokacin.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, wani kwamitin dake kunshe da kwararru ta fuskar soja ya yi bincike kan ginin da aka lalace, inda suka gano an saka bom ne a cikin bangon ginin, kuma sun ga alamu na fashewar bom din aka dana cikin mota. Kwararrun na hasashen cewa, wannan shi ne musabbabin lalacewar ginin.
Zuwa yanzu, sojojin Iraki sun rigaya sun tono gawarwaki 61 daga baraguzan ginin.(Murtala)