Kuma wannan shi ne karo na farko da bangarorin biyu suka hada kai wajen yaki da kungiyar IS, bayan sojojin sama na kasar Iraq sun kai hari kan dakarun kungiyar mai tsattsauran ra'ayin dake kasar Syria a watan Fabrairun bana.
Bugu da kari, cikin sanarwar da ofishin ba da jagoranci kan ayyukan hadin gwiwar ya bayar, an ce, a wannan karo, an kai hari kan kungiyar IS ta hanyar amfani da tsarin musayar bayanai dake tsakanin kasashe hudu da suka hada da Rasha, Syria, Iraq da kuma Iran.
A watan Satumba na shekarar 2015, bisa jagorancin kasar Rasha, kasashen hudu suka kafa wata cibiyar musayar bayanai a birnin Baghdad na kasar Iraq, inda za su dinga yin musayar bayanai kan harkokin kungiyar ta IS. (Maryam)