Haq yace, daga cikin adadin, sama da mutane 220,000 ne suka fice daga gidajensu a yammacin birnin na Mosul wadanda suke makwabtaka inda sojojin ke yin lugudan wuta daga bangaren yammaci tun a karshen watan Fabrairu. Ana cigaba da kai tallafi ga wadanda rikicin ya daidaita har ma da mutanen da aka kwace iko da yankunasu matukar dai damar hakan ta samu.
Bugu da kari, jami'an kula da marasa lafiya daga yammacin Mosul sun sake karuwa a yankin har ma sun kafa wasu sabbin asibitoci biyu a yankunan Adhba da Hamam al Alil, dake kudancin birnin Mosul.(Ahmad Fagam)