Haka kuma, bisa hasashen da aka yi, an ce, adadin karuwar tattalin arziki na kasashe masu tasowa a yankin Asiya da yankin Pacific gaba daya zai kai kashi 5 bisa 100 a shekarar bana, yayin da kashi 5.1 bisa 100 a shekara mai zuwa, wadanda za su fi adadin shekarar da ta wuce, watau kashi 4.9 bisa 100.
Bugu da kari, an ba da shawarar cewa, ya kamata kasashen da abin ya shafa su kyautata ayyukansu wajen gudanar da harkokin sha'anin kudi yadda ya kamata domin tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin zaman karko da kuma yadda ya kamta. (Maryam)