in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: NDRC ta alkawarta ci gaba da aiwatar da sauye sauyen bunkasa tattalin arziki
2017-04-28 09:51:19 cri
Hukumar samar da ci gaba da aiwatar da sauye sauye ta kasar Sin NDRC, ta alkawarta daukar karin matakai, wadanda za su kara daidaita matsayin tattalin arkin kasar Sin a wannan shekara ta 2017.

Wata sanarwa da aka fitar a jiya Alhamis, yayin taron masu ruwa da tsaki na kwanaki 2 da NDRCn ta gudanar, ta bayyana cewa sabon salon kawo sauyi a fannin bunkasar tattalin arzikin kasar, na cikin muhimman matakai da NDRC ke fatan ganin an aiwatar.

Matakan dai sun hada da yunkurin rage samar da kayayyakin da suka wuce bukata, da rage yawan gidajen da ba a saye, da rage wahalhalun kafawa ko gudanar da sana'oi, da kuma bunkasa sassan tattalin arziki masu rauni.

Sauran sassan sun hada da rage yawan matakan gudanarwa, da sauya tsare tsaren haraji, da na hada hadar cinikayya. Sai kuma sauya salon mallakar kadarori tsakanin gwamnati da sassa masu zaman kansu, da kara bude kofa ga karin sassa na tattalin arziki, tare da batun kare muhalli.

NDRC ta ce duk da cewa cikin watanni 3 na farkon wannan shekara an samu ci gaba mai armashi, a hannu guda rashin tabbas game da yanayin gudanar da tsare tsare, ya wajabta ci gaba, da zurfafa gyare gyare a fannonin tattalin arzikin kasar ta Sin.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China