Mahukunta a kasar Sin na ci gaba da daukar matakai, na hade tsarin bada lasisi, na bude harkokin cinikayya, da nufin kara kyautata muhallin cinikayya da bunkasa kasuwanni.
Da yake bayyana hakan yayin taron majalissar zartaswar kasar, firaminista Li Keqiang wanda ya jagoranci zaman a jiya Laraba, ya ce gwamnati na daukar matakai na sake sakarwa kasuwanni mara, matakin da zai baiwa 'yan kasuwa damar aiwatar da hada hada cikin sauki, tare da rage wahalhalu da ake fuskanta, yayin kafa sabbin harkokin kasuwanci. Mr. Li ya ce ko shakka babu, hakan zai fafada dama da 'yan kasuwa ke da ita, ta samar da hidima da ake bukata.(Saminu Alhassan)