Mahukuntan Najeriya sun alkawarta kaddamar da wani sabon shiri, wanda zai karkata akalar kasar ga amfani da na'urori masu kwakwalwa, wajen gudanar da harkokin da za su kara gina tattalin arzikin kasar.
Da yake tabbatar da hakan cikin wata sanarwa a jiya Laraba, ministan masana'antu, cinikayya da harkokin zuba jari Okechukwu Enelamah, ya ce nan da shekaru 10 masu zuwa, Najeriya za ta ci gajiya daga wannan tsari, wanda zai shigar da kimanin dalar Amurka biliyan 88 cikin ma'aunin tattalin arzikin ta na GDP, tare da samar da karin guraben ayyukan yi sama da miliyan 3, cikin shekarun 10 masu zuwa.
Sassan da wannan manufa za ta shafa dai sun hada da na biyan kudade ta na'urori, da fannin lafiya, da na bada ilimi da dai sauran su. Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin kasar ta yi amanar cewa, wannan tsari zai samar da dama ta amfana daga dumbin basira da matasan kasar ke da ita a sassa na fasaha, da raya tattalin arziki.
Ministan ya kara da cewa, da zarar an fara aiwatar da manufar, za a rage gibin da ake da shi a kasar, a fannin karancin samar da hidimomi masu inganci, tare da kara yawan damammaki na bunkasa tattalin arzikin kasar ta hanyoyi da dama.(Saminu Alhassan)