Hukumar samar da ci gaba da tsara sauye sauye ta kasar Sin ko NDRC a takaice, ta bukaci da a aiwatar da tsari, wanda zai bada damar kyautata samarwa, da amfani da makamashi a fadin kasar, ta yadda hakan zai yi daidai da yanayin da ake ciki na bukatar makamashi a kasuwannin duniya.
Cikin wata sanarwar da hukumar NDRCn ta fitar ta yanar gizo, ta ce nan da shekarar 2030, yawan makamashin da Sin ke amfani da shi, zai kai kwatankwacin tan biliyan 6 na kwal, wanda hakan ke kunshe cikin jadawalin shirin raya kasa na shekarun 2016 zuwa 2030. (Saminu Hassan)