Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, a lokacin wadannan ranakun hutu, bangaren yawon shakatawar kasar ya samu Yuan biliyan 79.1, kwatankwacin dala biliyan 11.5, lamarin da ke nuna karuwar kaso 16.2 cikin 100 a kan na shekarar da ta gabata.
Har ila yau, masu yawon shakatawa miliyan 134 ne suka ziyarci wuraren yawon shakatawa dake sassa daban-daban na kasar a lokacin hutun da aka kammala a jiya Litinin, adadin dake nuna karuwar kaso 14.4 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.
Ana samun bunkasar harkokin yawon shakatawa a kasar Sin ne a yayin da mahukuntan kasar ke kokarin canja akalar tattalin arzikin kasar daga dogara kan kayayyakin da ake fitarwa da harkokin manyan masana'antu zuwa ga tattalin arzikin dake bunkasa ta fuskar kayayyakin da ake amfani da su, da kirkire-kirkire da kuma bangaren samar da hidima.
Masharhanta na kallon bangaren yawon shakatawar kasar a matsayin ginshikin ci gaban harkokin tattalin arzikin kasar, duba da ribar da ake girba daga wannan sashe, kana daga harkokin otel-otel da sufuri da kuma harkokin samar da abinci. (Ibrahim)