Asusun IMF ya tabbatar da samun matsakaicin karuwar tattalin arzikin a yankuna ne, cikin bayanan dake kunshe cikin rahoton da ya fitar na baya bayan nan.
Sai dai kuma, IMF ya bayyana karuwar da za a samu na tattalin arzikin a wannan shekara da cewa wani hobbasa ne game da farfadowar tattalin arzikin yankunan, bayan da a shekarar da ta gabata aka samu karuwar 1.4 cikin 100.
IMF ta yi hasashen samun matsakacin karuwar tattalin arzikin kasar Afrika ta kudu da kashi 0.8 cikin 100 sakamakon tasowar farashin kayayyaki, da yanayin fari da ya saukaka da kuma fadada hasken lantarki a kasa.
A Najeriya ma hasashen na IMF ya nuna cewa tattalin arzikin kasar zai bunkasa da kashin 0.8 cikin 100 a shekarar ta 2017 a sakamakon farfadowar aikin hako albarkatun mai, da cigaban aikin gona, da kuma karuwar zuba jari da ake samu a kasar. Rahoton yace tattalin arzikin ya samu bunkasuwa da kashi 1.5 100 a shekarar 2016.