Mr. Rodlauer ya bayyana haka ne a jiya Juma'a, yayin taron manema labarai da aka yi mai taken "hasashen habakar tattalin arziki a yankin Asia-Pacific".
Ya kara da cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a cikin watanni uku na farkon shekarar nan ya wuce hasashen da Asusun ya fidda a baya, musamman ma la'akari da karuwar alkaluman GDP a cikin wadanan watanni, inda ya kai kashi 6.9 cikin dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara.
Shi ya sa, cikin sabon rahoton da Asusun ya fidda game da hasashen da aka yi kan tattalin arzikin kasashen duniya, aka canza adadin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin da aka yi a watan Juanirun bana daga kashi 6.5 zuwa kashi 6.6 cikin dari.
Har ila yau, ya ce gwamnatin kasar Sin ta riga ta dauki wasu matakai na hana karuwar farashin gidaje cikin sauri a wasu wurare na kasar, da kuma rigakafin matsalolin da za a iya fuskanta a fannin sha'anin kudi. (Maryam)