Bisa rahoton da aka gabatar, an ce, kasashe 7 wato Tanzania, Cote d'Ivoire, Habasha, Kenya, Mali, Ruwanda da Senegal dake yankin kudu da hamadar Sahara na Afirka, suna ta bunkasa tattalin arzikinsu. Kaza lika yawan mutanen dake kasashen 7 ya kai kashi 27 cikin dari bisa jimillar al'ummun yankin baki daya. Yayin da yawan GDPn nasu ya kai kashi 13 cikin dari, kana saurin bunkasuwar tattalin arzikinsu a kowace shekara tun daga shekarar 2015 zuwa 2017, ke karuwa da kashi fiye da 5.4 cikin dari.
Babban masanin tattalin arziki mai kula da yankin Afirka na bankin duniya Albert Zeufack ya bayyana cewa, kyautata yanayin zuba jari, da sa kaimi ga yin kwaskwarima don karfafa samar da kaya a masana'antun kasashen Afirka, da ma samar da yanayin tattalin arziki mai kyau, su ne dalilai na tabbatar da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin yankin. (Zainab)