Irin wadannan basuka sun tasarwa Yuan Tiriliyan 21.9, kwatankwacin dalar Amurka Tiriliyan 3.2, ya zuwa karshen watan Maris din da ya gabata, wanda hakan ke nuna karuwar kaso 17 bisa dari, idan an kwatanta da shekarar da ta gabata.
Wannan dai ci gaba a cewar PBOC, ya dara wanda aka samu a fannin manyan sana'o'i. Bankin dai na karfafa gwiwar bankuna da su kara samar da basuka domin tallafawa masu kananan sana'u, wadanda ke gamuwa da kalubale na samun rance cikin sauki. (Saminu Hassan)