A yayin jawabin nasa, shugaba Xi ya ba da shawarwari game da yadda za a gina makomar bil Adama cikin hadin gwiwa, da cimma moriyar juna, inda shawarwarin suka samu amincewa da yaba daga gamayyar kasa da kasa. Masanan kasa da kasa suna ganin cewa, shawarwarin da shugaba Xi ya bayar sun nuna hanyoyin da za a bi don neman ci gaba.
Masanin harkokin yankin arewa maso gabashin Asiya da kuma manufofin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai na kwalejin kimiyyar kasar Rasha Vladimir Matveev ya ce, kiran da aka yi na gina makomar bil Adama cikin hadin gwiwa domin samun ci gaban kasa da kasa cikin hadin gwiwa, ya samu amincewar galibin kasashen duniya
Shehun malamin jami'ar Nairobi ta kasar Kenya Garrishon Ikiara ya ce, jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi ya nuna cewa, kasar Sin ta mai da hankali sosai kan huldar dake tsakaninta da kasashe masu tasowa, kuma burin kasar Sin na gina makomar bil Adama cikin hadin gwiwa ya nuna matsayinta na babbar kasa mai tasowa a duniya, da kuma fatanta na shimfida zaman lafiya a fadin duniya, da kuma aniyar kasar ta yin hadin gwiwa da kasa da kasa domin cimma moriyar juna. (Maryam)